Shugaban hukumar kula da bakin haure a Libya Badredine Ben Hameed, ya ce an tasa keyar ‘yan Najeriyar ne karkashin wani hadin gwiwa tsakaninsu da hukumar kula na bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya OIM.
Akwai dai mata da dama cikin ‘yan ci-ranin da Libya ta taso keyarsu.
Wannan na zuwa bayan Libya ta taso keyar ‘yan kasar Cote d’Ivoire kimanin 150 a ranar Talata.
Kasar Libya dai ta kasance hanyar da ‘yan ci-rani ke ratsowa yawanci daga Nijar domin tsallakawa zuwa kasashen Turai.288